Isa ga babban shafi
caribbean

Daliban Najeriya sun koma sata a kasar waje

Daliban Najeriya da ke karatun likita a tsibirin Saint Vincent Grenadines na yankin Caribbean sun koma sata da damfara bayan sun shiga mawuyacin hali sakamakon rashin kudin alawus har na kusan shekaru biyu.

Daliban Najeriya da ke samun horo a aikin likita a tsibirin Saint Vincent and Grenadines sun shiga halin sata da damfara saboda rashin kudin alawus daga gwamnatin kasarsu
Daliban Najeriya da ke samun horo a aikin likita a tsibirin Saint Vincent and Grenadines sun shiga halin sata da damfara saboda rashin kudin alawus daga gwamnatin kasarsu Getty image/ David Sacks
Talla

A shekara ta 2013 ne, gwamnatin jihar Rivers da ke kudancin Najeriya ta dauki nauyin tura daliban da yawansu ya kai 16 a karkashin wani shirin tallafa wa dalibai.

Sai dai daliban da suka hada da maza da mata sun fara halin bera saboda rashin kudin siyan abinci ballantana biyan kudin makaranta.

Rahotanni sun ce, wasu daga cikinsu sun koma barace-barace a Majami’u yayin da aka fitar da su daga gidajen haya saboda rashin biyan kudin haya, lamarin da ya tirasasa musu kwana a kan tituna.

Tuni dai daliban suka fara aika sakwanni daban- daban ga gwamnatin jihar Rivers da kuma gwamanatin tarayyar Najeriya, inda suka bukaci agaji tare da fadin cewa, matukar ba a dauki matakin cire su daga kangin da suka shiga ba, to lallai hakan zai kara bata sunan Najeriya a kasashen ketare.

Daliban dai sun caccaki gwamnatin jihar Rivers kan yadda ta manta da su a kasarsa da ba tasu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.