Isa ga babban shafi
US

An kashe 'yan sandan Amurka hudu a Dallas

Wasu ‘yan kyare sun harbe jami’an ‘yan sandan Amurka hudu har lahira a lokacin wata zanga zangar nuna adawa da kisan bakaken fata biyu da ‘yan sandan suka yi.

Masu zanga zangar adawa da kisan bakaken fata a Dallas na Amurka
Masu zanga zangar adawa da kisan bakaken fata a Dallas na Amurka Laura Buckman / AFP
Talla

Har ila yau zanga zangar wadda aka gudanar a jiya Alhamis a birnin Dallas na Texas ta yi sanadiyar jikkatar ‘yan sanda bakwai kamar yadda hukumomi suka sanar.

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan sandan sun kashe Philando Castile a jihar Minnesota a ranar Laraba da kuma Alton Sterling a jihar Louisiana a ranar Talata.

Rahotanni na cewa, yanzu haka ‘yan sanda na kokarin shawo kan wani mutun dauke da bindiga mai sarrafa kanta a wani gareji, inda ya ke ta harbe harbe a cikin iska tare da yin barazar hallaka ‘yan sanda da dama kamar yadda shugaban ‘yan sandan na Dallas David Brown ya tabbatar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.