Isa ga babban shafi
US

Dan Sanda Farar Fata Ya Kashe Bakar Fata a Amurka

Jami'an ‘yan Sanda a Minnesota na kasar Amurka na binciken musabbabin kisan wani mutun bakar fata, da wani farar fata dan sanda ya yi, wanda akayi ta nunawa ta hotunan bidiyo, daya harzuka bakaken fata yin bore a fadin Amurka.

Budurwan mamacin Diamond Reynoldsa lokacin da take bada bayanin abinda ya faru.
Budurwan mamacin Diamond Reynoldsa lokacin da take bada bayanin abinda ya faru. REUTERS/Eric Miller
Talla

Bakar fatan mai suna Philando Castile, na cikin motar sa ne tare da wata budurwarsa a lokacin da ‘yan sanda suka tsayar da su.

Hotunan bidiyon da aka yi ta turawa jama'a ta kafofin sadarwan zamani, na nuna mamacin na kokarin ciro katin shaida ya nunawa ‘yan sandan har anji budurwar na cewa ‘yan sanda sun harbe shi a kafada yana kokari fito da takardan shaida ya nuna masu.

Kisan na zuwa ne bayan irin sa bada dadewa ba da wani farar fata dan sanda ya kashe wani bakar fatan mai suna Alton Sterling.

Sau da yawa dai ana zargin fararen fata ‘yan sanda da yiwa bakaken fata kisan gilla.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.