Kungiyar Taliban Ta Kashe 'Yan Sanda 30 a kasar Afghanistan
Kungiyar Taliban ta kashe akalla ‘Yan sanda 30 tare da raunana sama da 58 a wani harin bom da ta kai wa tawagar motocin da ke dauke da ‘Yan sanda a Kabul na kasar Afghanistan.
Wallafawa ranar:
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya bayyana harin da cewa laifin cin amanan biladama ne.
Wannan hari na zuwa ne mako daya bayan kashe wasu jami'an tsaro 14 dake kan hanyar su ta zuwa aiki a ofishin jakadancin kasar Canada.
Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce 'yan sandan na cikin jerin gwano na motocin su ne a yankin Kabul aka kai masu hari yau Alhamis.
Ganau sunce daya daga cikin maharan na tafe ne a kasa, yayin da wani ke cikin wata mota da aka shake ta da bama-bamai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu