Isa ga babban shafi
Boxing

Erdogan zai halarci Jana’izar Muhammad Ali

Shugaban Kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan da Sarki Abdallah na Jordan sun bayyana aniyarsu ta halartar jana’izar tsohon zakaran damben Boxing na duniya Muhammaed Ali da za a yi ranar juma’a a kasar Amurka.

Tsohon Shugaban Amurka George W. Bush na karrama Marigayi Muhammad Ali
Tsohon Shugaban Amurka George W. Bush na karrama Marigayi Muhammad Ali REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Bob Gunnell da ke Magana da yawun iyalan marigayin ne ya tabbatar da halartar shugabannin tare da bayyana cewa dubban mutane ake saran za su halarci jana’izar.

Wani jami’in fadar shugaban Amurka ya ce shugaba Barack Obama na nazari kan halartar jana’izar, da ake sa ran tsohon shugaban kasa Bill Clinton zai yi jawabi.

Fitattacen dan wasan fim Will Smith da kuma tsohon zakaran damben Boxing Lennox Lewis za su dauki akwatin gawar Muhammad Ali tare da wasu dangin shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.