Olympics- Likitoci sun gargadi Brazil kan Zika
Kasar Brazil tace bata da wani shiri na dage ko sauya inda za a gudanar da wasanni Olympics na bana, duk da wasikar da kwararaun likitoci na kasa da kasa 150 suka aike mata kan bukatar haka saboda Zika.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar, ta ce zata cigaba da amfani da shawarwarin hukumar lafiya ta duniya, da tayi watsi da kiran, cewa haka ba zai hana yaduwar cutar ta Zika ba, kuma, da wuya ma a samu yaduwarta a wannan lokaci
Kwararrun dai 150 na gani cewa akwai babban illar karban bakwanci wadanan wasanni a Garin Rio garin na Biyu da Cutar ta yadu.
Akalla jarirai 1,300 aka rawaito an haife su da nakasa a Brazil, tun fara yaduwar Cutar shekara daya da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu