Isa ga babban shafi
Serbia-ICC

Karadzic zai daukaka kara kan hukuncin ICC

Tsohon shugaban Sabiyawan Bosnia Radovan Karadzic, zai daukaka kara a game da hukuncin dauri na tsawon shekaru 40 da kotun duniya ICC ta yanke ma sa, bayan samun sa da laifin kisan kare dangi a yakin tsohouwar tarayyar Yugoslavia shekaru 20 da suka gabata. 

Radovan Karadzic da kotun ICC ta yanke wa hukuncin daurin shekaru 40.
Radovan Karadzic da kotun ICC ta yanke wa hukuncin daurin shekaru 40. Reuters / ICTY via Reuters TV
Talla

Daya daga cikin lauyoyin da ke kare Karadzic mai suna Peter Robinson ya ce, an yake hukuncin ne akan tunani kawai amma ba akan hujja ba.

Sai dai matan da suka rasa mazajensu sakamakon kisan kare dangin da Karadzic ya jagoranta, sun bayyana takaicinsu a game da wannan hukunci.

Karadzic mai shekaru 70 dai ya aikata laifukan yaki da aka kwatanta da mummunan yakin duniya na 2 kuma ya kasance daya daga cikin manyan shugabanin yankin Balkans da ya taba gurfana tare da fuskantar hukunci a gaban kotun ICC da ke birnin Hague bisa wannan laifin mai nasaba da yakin Bosnia da kashe mutane akalla  dubu 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.