Kotun ICC za ta yanke hukunci kan Karadzic
Wani lokaci a yau kotun hukunta manyan laifuka ta duniya za ta sanar da hukunci akan shugaban Sabiyawan Bosnia Radovan Karadzic, wanda kotun ta sama da aikata kisan kare dangi shekaru 20 da suka gabata a lokacin yakin tsohuwar tarayyar Yougoslavia.
Wallafawa ranar:
Karadzic tsohon soja mai shekaru 70 a duniya, an same shi da aikata laifuka har guda 11 masu nasaba da kisan mutane sama da dubu 100 tsakanin 1992-1995.
Ana kallan tuhumar da ake yi wa Karadzic na aikata laifun yakin da muhimmanci yayin da ya musanta zargin da ake yi ma sa tare da fadin cewa yana sa ran kotun za ta wanke shi daga zarge zargen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu