Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Paparoma Francis na ziyara a Afrika

Yau ne shugaban darikar katolika ta duniya Paparoma Francis ke fara ziyarar kasashen Afirka uku na kwanaki biyar inda zai fara isa kasar Kenya.

Shugabam darikar katolika ta duniya, Paparoma Francis
Shugabam darikar katolika ta duniya, Paparoma Francis REUTERS/Tony Gentile
Talla

Ziyarar za ta bai wa shugaban damar ganawa da shugabanin kasahsen Kenya, Uganda da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya tare da yi wa dubban mabiyansa jawabi da addu’oi.

Ana sa ran Paparoman zai gabatar da jawabai akan batutuwa da dama da suka hada da matsalar sauyin yanayi wanda za a gudanar da taro a kai a birnin Paris na Faransa.

A karo na uku kenan da shugaban mabiya katolika ta duniya ya kai ziyara nahiyar Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.