Jirgin fasinjan Rasha ya yi hatsari dauke da mutane 224
Jami’an agaji sun soma isa a inda wani jirgin saman fasinjan kasar Rasha ya yi hatsari a yankin Sinai na kasar Masar a safiyar asabar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ofishin firayi ministan Masar Sherif Ismail, ya ce jirgin ya tashi ne daga wurin shakatawa na Sharm El-Cheick da ke Masar kan hanyarsa ta zuwa Saint-Petersbourg na Rasha dauke da fasinjoji 217 tare da ma’aikatan jirgin 7 kafin daga bisani sadarwa tsakanin matuki jirgin da jami’an kula da zirga-zirga ta tsinke.
Kawo yanzu babu tabbas a game da adadin mutanen da suka hallaka ko kuma suka tsira da rayukansu a wannan jirgi kirar Airbus A-321.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu