Isa ga babban shafi
Faransa-Malaysia

An ci gaba da binciken sassan jirgin saman kasar Malaysia mai lamba MH370

Yau Lahadi aka ci gaba da neman buraguzan jirgin saman kasar Malaysia mai lamba MH370, da yayi batan dabo a tsibirnin Reunion na kasar Faransa, dake kan tekun India, bayan dakatar da aikin a ranar Juma’a, saboda rashin kyawun yanayi.Suma mahukuntan Mauritius, dake makwabtaka da yankin, sun fara bincike ko za a sami wasu sassan jirgin a yankunan kasar.  

Jirgin aikin binciken jirgin kasar Malaysia na MH370
Jirgin aikin binciken jirgin kasar Malaysia na MH370 AFP PHOTO / RICHARD BOUHET
Talla

Jirgin saman na binciken katafaren yankin, da yakai murabba’in KM 5,300, inda kuma sauran kanana masu bincike ke zuwa gabar ruwan, don bayar da tasu gudunmawarsu a aikin binciken.
Jami’a yankin sun ce wani jirgin sama na zagaye yankin, yayin da ma’aikata ke tattaki a kasa, inda suke fatan ganin wani abinda zai kaisu ga inda jirgin ya fadi, kafin a tayar da jiragen sojan ruwa zuwa wajen.
A karshen watan Yulin da ya gabata aka tsinci wani bangaren jirgin, da kuma Firaministan kasar ta Malaysia ya bayar da tabbacin shine yayi batan dabo ranar 8 ga watan Maris din shekarar bara, a lokacin da yake dauke da 239.
Ko makon da ya gabata sai da mahukuntan kasar ta Malaysia suka tafka kuskure, inda suka bayyana cewa an gano wata kujera da tagar jirgin kirar Boeing 777, amma daga bisani jami’an kasar Faransa suka ce ba haka bane.
Tun cikin makon daya gabata, lokacin da aka gano fiffiken jirgin, klafafen yada labaru daga sassan duniya ke ci gaba da yin tururuwa zuwa garin Saint-Andre mai kimanin mutane dubu 50, inda aka yi tsuntuwar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.