Amurka
Amurka ta soki Rasha saboda ziyarar Assad
Fadar Shugaban kasar Amurka ta yi tir da irin tarbar da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi wa shugaba Bashar al Assad na Syria, inda ta bayyana shakku kan matsayin Rasha na warware rikicin siyasar kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Mai Magana da yawun fadar Eric Shultz ya ce yadda shugaba Assad ya yi amfani da makami mai guba kan jama’ar kasarsa, bai dace a masa irin wannan tarbar ba.
A ranar talatar da ta gabata ne Assad ya gana da Putin a birnin Moscow, inda ya yaba da hare haren saman da Rasha ke kaddamar wa kan mayakan IS a Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu