Isa ga babban shafi
Palestine

An daga tutar Falasdinu a MDD

A karon farko a tarihi, an daga tutar Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya a ranar laraba, lamarin da ya karfafa mata gwiwa a gwagwarmayar neman zama kasa mai cin gashin kanta.

A ranar laraba aka daga tutar Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya.
A ranar laraba aka daga tutar Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya. GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP
Talla

Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ne ya daga tutar mai launin ja da baki da fari da kuma kore yayin da ya gabatar da jawabi a cikin farin ciki, inda ya ce, an kafa tarihi a wannan ranar kuma ya bukaci Falasdinawa da su daga tutarsu a duk inda suke, wadda ita ce alamar gwagwarmaya da kuma yancinsu.

Sai dai wannan damar da Majalisar Dinkin Duniya ta bai wa Falasdinu, ya kona ran Isra’ila yayin da Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana jawabin Mahmud Abbas a matsayin munafurci tare da kiran sa mayaudari, mai tinzira jama’a.

Sai da aka samu amincewar kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 119 kafin a daga tutar ta Falasdinu.

To sai dai kasar Amurka da Australia da Israila sun kaurace wa zaben, inda Amurka ta ce hakan ba zai taimaka wa kokarin zaman lafiya da ake so a tsakanin Israil da Falasdinu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.