Sabon rikici ya barke a Masallacin birnin Kudus
Sabon rikici ya barke tsakanin Falasdinawa da Jami’an tsaron Isra’ila a safiyar yau litinin a harabar masallacin birnin Kudus.
Wallafawa ranar:
Jami’an ‘Yan Sanda sun yi ta wurga barkonon tsohuwa yayin da matasan Falasdinawa da suka yi alkawarin kare Masallacin na Kudus, suka yi ta wurga duwatsu.
Rohotanni sun ce, jim kadan da fara rikicin, ‘Yan Sanda sun tursasa wa Musulman da suka yi sallar asuba a Masallaci fice wa daga cikinsa yayin da kuma aka rufe dukkanin kofofin da Musumai ke bi domin shiga cikin Masallacin.
Tuni dai Hukumomin Isra’ila suka baza dimbin jami’an tsaro a gabashin birnin na Kudus har zuwa zagayen masallacin a daidai lokacin da yahudawa ke shirin gudanar da bukukuwan sallarsu ta shekara shekara mai suna Sukkot.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu