Isa ga babban shafi
Isra'ila

Rikici ya barke a Masallacin birnin Kudus

Rikici ya barke tsakanin Sojojin Isra'ila da Falasdinawa a harabar Masallacin Al-Aqsa dake birnin Kudus bayan sojojin sun kutsa kai cikin Masallacin a yau lahadi.

Masallacin Al-aqsa na birnin Kudus na daya daga cikin manyan Masallatan da Musulmai ke ji da su a duniya bayan Masallatan Makkah da Madina
Masallacin Al-aqsa na birnin Kudus na daya daga cikin manyan Masallatan da Musulmai ke ji da su a duniya bayan Masallatan Makkah da Madina REUTERS/Ammar Awad
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa Sojojin sun jefa hayaki mai sa hawaye a lokacin da suke  kokarin shiga cikin masallacin domin kama wadansu Falasdinawa da suka ce suna wurgo duwatsu daga cikin masallacin.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa Sojojin sun yi barna a cikin masallacin, to sai dai sun musanta haka tare da fadin cewa kawai sun rufe kofofin masallacin ne domin kulle masu wurge wurgen duwatsun.

Tuni dai hukumomin Isra’ila suka rufe harabar masallacin sakamakon rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.