Isa ga babban shafi
Sudan

Afrika ta kudu za ta sake budewa Al Bashir kofar shiga kasar

Shugaban Kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya ce shugaban Sudan Omar Hassan al Bashir zai sake ziyartar kasar wajen halartar taron kungiyar hadin kai da China, ta da kunshi kasahsen Afirka 50 da za a gudanar a watan Disamba.

Shugaban Sudan Omar al-Bashir
Shugaban Sudan Omar al-Bashir Reuters
Talla

Shugaba Zuma ya shaidawa jami’an diflomasiya cewar, Sudan na daga cikin kasashen Afirka da ke cikin kungiyar aminnan China kuma zata samu wakilci a taron.

Shugaban na Afrika ta kudu yace suna nazari akan bukatar bayanai da kotun duniya ta bukata kan kasa kama shugaba al Bashir a lokacin da ya halarci taron Tarayyar Afrika.

Masu shari’a a kotun ICC da ke hukunta laifukan yaki a duniya sun bukaci bayani ne daga Afrika ta kudu akan dalilin rashin cafke shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir a lokacin ya kai ziyara a kasar a watan Yuni.

Kotun kuma ta ba Afrika ta kudu wa'adi zuwa 5 ga watan Oktoba ta bayyana dalilin rashin kame al Bashir.

Afrika ta kudu dai na cikin mambobin kotun ICC, amma yanzu kasar tace za ta yi nazari akan wakilcinta a kotun saboda batun al Bashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.