Isa ga babban shafi
Africa ta Kudu

Muhawara kan tsige Jacob Zuma a Afrika ta Kudu

Yau Talata ‘yan majalisun kasar Afirka ta kudu za su fara tafka mahawara kan bukatar tsige shugaban kasar Jacob Zuma da ake zargi da kin kama shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir lokacin da ya ziyarci kasar.

Shugaban kasar Africa ta Kudu, Jacob Zuma.
Shugaban kasar Africa ta Kudu, Jacob Zuma. Reuters/Sumaya Hisham
Talla

Jam’iyyar Democratic Alliance ce ta gabatar da bukatar, wanda ta zargi shugaba Zuma da kin aiwatar da dokar kasar.

Shugaba Zuma wanda ke mayar da matarni a game da zargin da ‘yan adawa a majalisar dokokin kasar ke yi masa dangane da yadda ya bari Al Bashir ya sulale daga kasar a lokacin taron koli na kungiyar Tarayyar Afirka, ya ce shugaban na Sudan na da cikakkiyar kariya, domin kasancewar bakon kungiyar Tarayyar Afirka.

Kuma bashi da hurumin kama shugaba al Bashir saboda ba shine ya gayyace shi ba.

Jacob Zuma ya ce, Al Bashir ya shigo Afirka ta kudu ne ba wai bisa gayyatar kasar ba, sai dai a matsayinsa na bakon kungiyar AU, kuma kamar sauran shugabannin kasashen dole ne a ba shi kariya a tsawon lokacin da ya ke a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.