Isa ga babban shafi
Turai

WHO ta yi gargadi kan cututuka tsakanin bakin haure

Hukumar lafiya ta Majalisar dinkin duniya duniya WHO, ta bukaci kasashen Turai da su mayar da hankali kan barazanar da ake samu a bangaren lafiyar al-umma sakamakon matsalar kwararar baki ‘Yan gudun hijira, yayin da kuma ta nemi a taimakawa bakin.

Reuters/路透社
Talla

Daraktar hukumar lafiya a Kasashen Turai, Zsuzsanna Jakab ta bayyana cewa a yayin da ‘yan gudun hijirar ke ci gaba da yin kaura, dole ne daukacin kasashen turai da ‘yan gudun hijirar su hada kai domin fuskantar barazanar da ake samu a fannin lafiyar al-umma.

Jakab ta fadi haka ne bayan wani taro da hukumar lafiyar ta gudanar a babban birnin Vilnius na Kasar Lithuania.

A cikin wannan shekarar ka dai sama da ‘Yan gudun hijira dubu 430 ne suka kauracewa kasashenen su sakamakon yake-yake da talauci.

Hukumar lafiyar ta duniya dai ta ce akasarin ‘yan gudun hijirar da suka hada da kananan yara da tsofaffi na dauke da kannanna raunuka a jikinsu harma da matsalar karancin ruwa da ke addabar su.

Hukumar lafiyar ta kuma yi watsi da cece-kucen da ake yi na cewa ‘Yan gudun hijirar za su yada cututtuka tsakanin al-ummar nahiyar Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.