Guatemala na gudanar da zaben shugabancin kasa, mai cike da ja in ja.
Sama da mutane miliyan 7,5 yan kasar Guatemala ne a yau lahadi aka gayyata su halarci runfunar zaben sabon shugaban kasar, a dai dai wannan lokaci da kasar ke fama da matsalar cin hanaci, mako guda bayan murabus din da shugaban kasar ya yi, kafin a zarce da shi a kurkuku saboda dalilan cin hanci
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rumfunan zabe sun buda kofofinsu , a wannan kasa dake tsakkiyar nahiyar Latin Amruka, mai kunshe da al’umma miliyan 15 da doriyar dubu 800 da misalin karfe 7 na safiyar yau lahadi, zasu kuma rufe da misalin karfe 6 na yamma, kafin fara samun sakamakon farko na zaben da misalin karfe 9 zuwa 3 na dare.
A jiya assabar dai dubban yan kasar ne, suka gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewa da zaben, da suka ce an shirya shi ba a kan ka’ida ba
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu