Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

Gaye ya mayar da martini bayan tube shi jekadan MDD a Afrika ta tsakiya

Babban Jekadan Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Babacar Gaye wanda aka tube daga mukaminsa sakamakon batun yin lalata da mata da ake zargin dakarun Majalisar da aikatawa, ya ce bai yi mamaki a game da matakin tube shi da Ban Ki-moon ya dauka ba.

Janar Babacar Gaye
Janar Babacar Gaye radiookapi.net
Talla

Gaye ya shaidawa RFI cewa ra’ayin shi bai sha bamban da na Ban Ki-moon ba, wanda ya bayyana matukar bacin ransa dangane da matsala yin lalata da mata da dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar Dinkin Duniya suka aikata.

Ban ki-moon ya bukaci a dora wa hukumar gudanarwa ta Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya alhakin yin sakaci har aka sami wannan matsala.

Gaye ya ce ba abin mamaki ba ne idan an diga ayar tambaya dangane da alhakin da ya rataya a wuyan jagorar hukuma.

Tube Gaye dai na zuwa ne bayan kungiyar Amnesty ta zargin Sojin Majalisar Dinkin Duniya da yi wata yarinya ‘yar shekaru 12 fyade.

Babacar Gaye dai Janar ne a rundunar Sojan Senegal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.