Isa ga babban shafi
China-Faransa

China ta kulla cinikin sayen Jiragen Airbus

Katafaren kamfanin kera jiragen saman na Nahiyar Turai Airbus, na kasar Faransa ya kulla yarjejeniyar cinikin sayarwa kasar China da jiragensa samfarin A330 guda 75 a kan adadin kudin da suka kai Dalar Amurka biliyan 18.

Firimiyan China Li Keqiang a fadar François Hollande a Paris.
Firimiyan China Li Keqiang a fadar François Hollande a Paris. Reuters
Talla

Yarjejeniyar ta shafi kwangiloli 45 da aka kammala, da kuma wasu guda 30 da ke kan hanya, an kuma rattaba hannu a kan wannan ciniki ne tsakannin shugaban kamfanin na Airbus, Fabrice Brégier, da shugaban sashen da ke kula da sayen jiragen sama na kasar China (CAS), a lokacin wata ziyara ta tsawon kwanaki uku da Firimiyan China Li Keqiang ya kai a kasar Faransa.

Ana sa ran cim ma yarjeniyoyi 53 a lokacin wannan ziyara ta Firimiyan China a Faransa, wanda a yau Laraba zai ziyarci birnin Marseille da ke kudanci, kafin gobe Alhamis ya zarce zuwa Toulouse da ke yankin kudu maso yammaci kasar Faransa tare da kai ziyara cibiyar kamfanin kera jiragen sama na Airbus.

Baya ga wannan ciniki da China ta kulla da kamfanin na Airbus, ana sa ran ta sake kulla ciniki da katafaren kamfanin samar da makamashin nan na Alstom, da kuma kamfanin sufurin jiragen ruwa na CMA-CGM na uku mafi girma a duniya, da kamfanin Engie (GDF Suez)

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.