Isa ga babban shafi
IS-Iraq

Mayakan IS sun kira Jihadi a cikin Azumi

Mayakan Kungiyar IS da ke da'awar kafa daular Islama sun bukaci al’ummar Musulmi su kaddamar da Jihadi domin mutuwar shahada cikin watan Azumin Ramadan mai alfarma. Kakakin Kungiyar ne Abu Muhammad al Adnani ya yi wannan kiran a cikin wani sako a Intanet.

Mayakan IS da ke da'awar Jihadi a Syria da Iraqi
Mayakan IS da ke da'awar Jihadi a Syria da Iraqi REUTERS
Talla

Adnani ya sanar da yin afuwa ga mutanen da ke yaki da su a lardin Anbar na Iraqi tare da yin kira ga wadanda suka gudu su dawo gidajensu.

Adnani ya ce Jihadi kawai ke sa mutum kusanci da Allah, saboda haka yana kira ga magoya bayansu da su gagaguta Jihadi a cikin watan Ramadan.

Mayakan IS sun karbe ikon garuruwa da dama a Iraqi tun lokacin da suka kaddamar da yaki a watan yunin Bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.