Isa ga babban shafi
MYANMAR

Japan ta taimaka wa 'yan Rohingya da makuddan kudade

Gwmanatin kasar Japan ta ware dala milyan uku da rabi domin taimaka wa ‘yan kabilar Rohinga wadanda musulmai ne tsiraru amma ake ci gaba da kora daga kasar Myanmar ba tare da an samu wata kasar da za ta karbe su ba.

'Yan kabilar Rohingya a wani sansani.
'Yan kabilar Rohingya a wani sansani. Reuters
Talla

Ministan harkokin wajen Japan Fumio Kishida, ya ce kasar za ta yi iya kokarinta domin shawo kan kasashen yankin Asiya cikinsu kuwa har da kasar ta Myanmar domin samarwa ‘yan kabilar ta Rohingya marasa rinjaye makoma tagari.

Za a dai yi amfani da wadannan kudade ne domin sayen abinci da kuma matsugunai ga wadannan mutane da a halin yanzu ke rayuwa a cikin kananan kwale-kwale kan teku sakamakon rashin samun kasar da za ta karbe su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.