Isa ga babban shafi
G7-Najeriya

An shiga rana ta biyu a taron kasashen G7

Wannan litinin ita ce ranar ta biyu kuma ta karshe a taron G7 na kasashen duniya bakwai masu karfin tattalin arziki da ke gudana a Elmau da ke kasar Jamus.

Shugabannin G7 a 'Elmau, kasar Jamus 7ga watan Yunin  2015.
Shugabannin G7 a 'Elmau, kasar Jamus 7ga watan Yunin 2015. REUTERS/Alain Jocard/Pool
Talla

Taron wanda a lokacinsa shugabannin kasashen ke tattauna batutuwan da suka shafi duniya, a wannan karo, rikicin Rasha da Ukraine, matsalar basusukan da ta dabibaye kasar Girka, yaki da ayyukan ta’addanci a duniya, sauyin yanayi……na daga cikin muhimman batutuwan da shugabannin suka fi mayar da hankali a kai.

Har ila yau taron na bana ya gayyaci wasu daga cikin shugabannin kasashen duniya, da suka hada da Muhammadu Buhari na Najeriya da Jacob Zuma na Afirka ta kudu.

A yau litinin an tsara Buhari zai gabatar da jawabi a gaban shugabannin manyan kasashen na duniya, kuma batun Boko Haram zai kasance daya daga cikin muhimman batutuwan da zai tabo kamar dai yadda majiyoyi suka bayyana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.