Zazzabin cizon Sauro na cigaba da yin kisa a duniya-MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, har yanzu akwai mutane akalla dubu 600 da ke rasa rayukan su sakamakon zazzabin cizon sauro wato Malaria, inda ta bukaci kara kaimi domin yaki da cutar.
Wallafawa ranar:
Majalisar ta sanar da hakan ne bayan hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, jan kafa dangane da samar da wadatattun magungunan zazzabin cizon sauran na ta’azzara matsalar magance cutar.
Wani babban Jami’i a hukiumar lafiya ta MDD, Richard Cibulskis ya shaidawa taron manema labarai a birnin Geneva da ke Switzerkland cewa, sun taka muhimmiyar rawa wajan yaki da zazzabin cizon sauran.
Cibulskis ya kuma ce, kamuwa da cutar a duniya ya ragu da kashi 30 cikin 100, lamarin da yasa aka samu raguwa kashi 40 cikin 100 na wadanda ke rasa rayukansu saboda cutar.
To sai dai duk da wanna nasarar, hukumar lafiyar ta duniya ta ce, har yanzu ana bukatar kara kaimi dangane da yaki da cutar
Sanarwa na zuwa ne, adai-dai lokacin da ake shirin gudanar da ranar zazzabin cizon sauro ta duniya, 25 ga watan Afrilu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu