Isa ga babban shafi
Amurka-Cuba

Amurka ta gana da Cuba a Panama

Ministocin harakokin wajen Amurka da Cuba sun yi wata ganawa a Panama, inda wannan ne karon farko da manyan Jami’an diflomasiyar kasashen biyu suka gana tun 1958 da aka kawo karshen yakin cacar-baka.

John Kerry na Amurka yana tabewa da Bruno Rodriguez na Cuba a Panama
John Kerry na Amurka yana tabewa da Bruno Rodriguez na Cuba a Panama REUTERS/U.S. State Department/Handout
Talla

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ya gana ne da takwaransa na Cuba Bruno Rodriguez a jiya Alhamis, ganawar da ake gani mai dimbin tarihi tsakanin kasashen biyu.

Ana sa ran Shugaban kasar Amurka Barack Obama zai gana da takwaransa na Cuba Raul Castro a karon farko bayan kawo karshen takun sakar da aka kwashe sama da shekaru 50 ana yi tsakanin kasashen biyu.

Tuni Obama da Castro suka isa Panama don halartar taron kasashe 35 na Latin da za a kwashe kwanaki biyu ana yi.

Wannan ne karon farko da Cuba ta halarci taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.