Isa ga babban shafi
Amurka

An bukaci Falasdinawa su biya wasu Amurkawa diyya

Wata Kotu a Amurka ta bukaci shugabannin Falasdinawa su biyya diyyar kudi Dala miliyan 218 ga wasu Amurkawa shida da aka kai wa hare hare dabam dabam a Isra’ila daga shekarar 2002 zuwa 2004. Ma su taimakawa Alkalin Kotun New York shawara ne suka bukaci a biya diyyar.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas REUTERS/Mohamad Torokman
Talla

Kuma sun ce sun samu Hukumar Falasdinawa da Kungiyar fafutikar ‘yancin Falasdinu da laifufuka 25 da suka hada da kashe mutane 33 tare da raunata 390.

Sai dai lauyan Falasdinawan ya ce bai dace a kama shugabanin da laifin da wasu marasa hankali suka yi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.