Isa ga babban shafi
Gaza

MDD ta dakatar da aikin gyran gidajen mutanen Gaza

Hukumar da ke kula ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana dakatar da aikin gyaran gidajen mutanen Gaza da Isra’ila ta tarwatsa a hare haren da ta kai wa Falasdinawa a shekarar da ta gabata. Hukumar tace ta dakatar da aikin ne saboda masu bayar da tallafin sun ki bayar da tallafin.

Gidajen Mutanen Gaza da Isra'ila ta ruguza
Gidajen Mutanen Gaza da Isra'ila ta ruguza Photograph: Thomas Coex/AFP/Getty Images
Talla

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar tace ta kashe dukkanin kudaden da ke hannunta ga aikin gyran gidajen na mutanen Gaza.

Kimanin kudi sama da biliyan biyar aka yi alkwalin samarwa a taron Gaza da aka gudanar a birnin Alkahira na Masar a watan Oktoba, amma hukumar tace har yanzu babu wani tallafin kudi da ya isa zuwa Gaza.

An shafe  tsawon kwanaki 50 Isra'ila na luguden wuta a Gaza.

Akalla Falasdinawa 2,140 ne Isra’ila ta kashe yawancinsu fararen hula yayin da kuma Sojojin kasar 64 suka mutu a hare haren da Hamas ta kai a yankunan Yahudawa.

Kungiyar kare hakkin bil’adama Amnesty International tace kazaman hare-hare da Isra’ila ta yi ta kai wa a yankin Gaza, laifukan yaki ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.