Isa ga babban shafi
Ebola

Masana harhada magungunna sun hadu a Geneva kan maganin Cutar Ebola

Masana harkokin lafiya na Duniya na hallartan taro a Geneva domin tafka muhawara kan sabbin magungunan Cutar Ebola da kamfanoni daban-daban suka harhada

DR
Talla

Kungiyar lafiya ta Duniya ta fadi cewa taron na yau, na daga cikin kokarin da ake yi domin samo mafita daga wannan Cuta da ta riga ta kashe mutane akalla dubu 8 da 200.

Kungiyar ta ce maharta taron sun hada da jami’an kiyon lafiya na Duniya, kamfanonin harhada magunguna, da wakilan Gwamnatoci musamman daga kasashen da cutar ta yiwa illa, haka kuma za su duba lamurran kudaden magungunan a kasuwanni.

Kungiyar lafiya ta Duniya bata ce ga maganin cutar ba, illa iyaka a garzaya da wanda ake kallon sun kamu zuwa wuraren da aka kebe.

Talata da ta gabata ne dai aka fara gwajin wasu magungunan da kamfanin Johnson and Johnson suka gafatar a Britaniya.

Kazalika akwai wani maganin da Glaxosmith na Britaniya ya gabatar, da ake gwajin a kasar Switzerland da Mali da Britaniya da Amirka.
Akwai kuma wani maganin da wani kamfanin kasar Canada ya yi da ake gwajinsa a Amirka, Canada Jamus da Gabon.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.