Isa ga babban shafi
Amurka-AFIRKA

Obama ya gana da matasan nahiyar Afirka a Washington

A jiya litinin a birnin Washington na kasar Amurka, shugaba Barack Obama ya gana da wasu matasa 500 da suka fito daga nahiyar Afirka, inda ya karfafa masu guiwa dangane da yadda nahiyar za ta samar wa kanta ci gaba a fannoni daban daban na rayuwa.

Matasan Afirka na ganawa da Obama
Matasan Afirka na ganawa da Obama
Talla

Ganawar wadda aka shirya kafin taron shugabannin Afirka da Obama a nan gaba kadan domin tattauna batutuwa da dama da suka shafi hulda tsakanin bangarorin biyu, a lokacinta Obama ya ce kafin shekara ta 2016, matasa da ke da kware a fagen kasuwanci da masana’atu da yawansu ya kai dubu daya ne za a bai wa damar zuwa Amurka domin yin karatu a cikin jami’o’in kasar.

Amurka dai na taimakawa kasashen Afirka a fannoni da dama da suka hada da tsaro, ilimi, tattalin al’adu da dai sauransu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.