Isa ga babban shafi
Amurka

Sojan Amurka ya kashe kansa bayan harbe mutane uku

Wani sojan kasar Amurka ya harbe mutane uku sannan daga baya ya harbe kansa, a wani sansanin soji dake Yankin Fort Hood na Jihar Texas, lamarin da har ila yau ya raunata wasu mutane 16.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama
Shugaban kasar Amurka Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Bayanai na nuna cewa dukkanin wadanda lamarin ya rutsa da su sojoji ne.

Rahotanni sun ce sojan, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya taba aikin wanzar da zaman lafiya a Iraqi a shekarar 2011, kuma rundunar sojin kasar ta Amurka ta tabbatar da cewa yana fama da alamun tabin hankali da matsalar kadaici.

Yanzu haka bayanai na nuna cewa mutane hudu daga cikin mutane 16 da suka samu raunuka na cikin mawuyacin hali. 

“Babu wata alama da ke nuna cewa wannan lamari na da alaka da ta’addanci, amma dai ba za mu kawar da dukkanin zato ba.” Kwamandan sasanin Laftanar Janar Mark Milley ya gayawa ‘yan jarida.

Rahotanni sun ce sojan ya yi amfani ne da wata karamar bindiga wacce ya yi fasakwaurinta zuwa cikin sansanin inda ya shiga wani ginin da ake kula da marasa lafiya ya bude wuta.

Sannan daga baya kuma ya shiga wata mota ya ci gaba da harbi, inda daga karshe ya shiga wani gini ya kuma harbe kansa.

A dai shekarar 2009 makamancin wannan lamari ya auku a cikin wannan baraki na soja.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.