Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Fafaroma Francis ya jagoranci bikin Kirsemeti a karon farko

Shugaban mabiyar darikar Katolika na Duniya Fafaroma Francis na daya, a karo na farko ya jagorancin addu’o’I dangane da raya daren Kirismeti a St Peters Basilica da ke Vatican, inda ya yi addu’o’I ga mutanen da rikici ya shafa da matsalar tattalin arziki.

Shugaban mabiyar darikar Katolika na Duniya Fafaroma Francis na daya, a karo na farko ya jagorancin addu’o’I dangane da raya daren Kirismeti a St Peters Basilica da ke Vatican.
Shugaban mabiyar darikar Katolika na Duniya Fafaroma Francis na daya, a karo na farko ya jagorancin addu’o’I dangane da raya daren Kirismeti a St Peters Basilica da ke Vatican. REUTERS/Tony Gentile
Talla

Fafaroma Francis ya bayyana cewa wadanda ake neman tauyewa hakkokinsu, suna a matsayin mutanen farko da suka fi karbar sakwannin Ubangiji, yana mai yin kira ga Kiristoci a duk inda suke a duniya, da su cire tsoro daga zukatansu, sannan su kasance masu aiki da gaskiya da kaucewa aikata zalunci a rayuwarsu.

Fafaroma ya share tsawon sa’o’I biyu yana jagorantar addu’o’in a jajibirin Kirsemeti. Inda a yau ne zai gabatar da wasu addu’o’in a game da zagayowar ranar ta haihuwar Yesu da suke bautawa.

Akwai Babban limamin Mujami’ar Bethlehem a birnin Kudus Fuad Twal da ya jagoranci Addu’oi inda Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya halarta.

A cikin addu’o’insa, Twal ya tuna rikice rikicen da ke faruwa a kasashen Afrika da bala’in guguwar da aka samu a Philippines da kuma halin da ake ciki a kasashen Masar da Iraqi da Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.