Isa ga babban shafi
Waiwaye Adon Tafiya

Yadda rikicin siyasar Amurka ya shafi tattalin arzikin duniya

Wallafawa ranar:

A kasar Amurka, a yanzu dai dubban mutane ne suka koma a wuraren ayyukansu, bayan da shugaba Barack Obama ya amince da dokar da ke bayar da damar sake bude ma’aikatun gwamnatin kasar, da suka yi fiye da makwanni biyu a rufe saboda da sabanin da aka samu a game da aiwatar da dokar kasafin kudin kasar a Majalisa. Bayan da aka kawo karshen wannan kiki kakar, lamarin da ya yi sanadiyya jefa tattalin arzikin kasar cikin rudani, yanzu masana na cewa lamarin ya yi sanadiyyar kasar ta yi asarar kudaden da suka kai Dalar Amurkan $20 billion, a bangaren kayayyakin da ake kerawa akasar, wato GDP.Wannan, da ma wasu batutuwan da suka biyo bayan waccan matsalar ne abubuwan da Nasiruddeen Muhammad ya yi nazari a shirin Kasuwa a kai Miki Dole na wannan makon.Ayi saurare lafiya. 

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Larry Downing
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.