Isa ga babban shafi
Brazil

Kanfunnan kasashen Turai da China sun sami aikin tono man kasar Brazil

Wasu kamfunnan man kasashen Duniya sun yi hadin gwiwa, inda suka sami mallakar rijiyoyin man kasar Brazil da ake kira Libra. Yarjejeniyar ta kunshi tono man da aka gano a yankin kasar ta Brazil a cikin tekun Atlantika, shekaru 6 da suka gabata.Kamfanonin kasar China CNOOC da CNPC, na hadin gwiwa da Shell na Britaniya, gami da Total na kasar Faransa, inda suka hade da kamfanin Petrobras na gwamnatin Brazil don mallakar rijiyoyin main a Libra.Yarnjejeyar ta tsawon shekaru 35, ta baiwa kamfanin Petrobras ikon mallakar kashi 40 cikin 100 na man da za a tono yayin da shell da Total ke da kashi 20, su kuma CNOOC da CNPC za su sami kashi 10 kowannen su.Kamfanonin kashen wajen, da Petrobras na hadin gwiwar, da shine kawai da zai samar wa Brazil a kalla kashi 41 cikin 100 na man da za tono a wannan wuri, da ke da kimanin ganga miliyon dubu 12.Kamfanoni 10 ne suka yi gasar neman mallakin rijiyoyin, amma ba 1 daga Amurka.Kamfanonin Amurka na tunanin shigar Petrobras cikin lamarin zai baiwa hukumonin kasar Brazil damar tsoma baki a harkar man fiye da kima. 

wani ma'aikacin kamfanin total na Faransa
wani ma'aikacin kamfanin total na Faransa Total.com
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.