Isa ga babban shafi
Mexico

An kama wani mai safarar kwayoyima Mexico

‘Yan sanda a kasar Mexico sun cafke wani mutum mai safarar miyagun kwayoyi wanda ake kuma zargi da hanu a wasu kashe kashe da aka na sama da mutane 350 da aka boyesu gawawwakinsu a wasu kabarurruka a kasar.‘Yan sanda sun kama Mario Nunez Mezam, mai shekaru 39 a yankin Ciudad Juarez dake kusa da kan iyakar kasar ta Mexico da Jihar Texas dake Amurka, inda suka ce sun kama Mario ba tare da ya nuna wata Turjiya ba.Lamarin kashe kashen da ked a alaka da safarar miyagun kwayoyi lamari ne da ya zama ruwan dare a kasar ta Mexico.A wasu lokutan har ‘yan sanda suna rasa ransu sakamakon fito na fiton ca suke yi da masu safarrar kwayoyin, da ke amfani da muggan makamai. 

Shugaban kasar Mexico Peña Nieto
Shugaban kasar Mexico Peña Nieto Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.