Isa ga babban shafi
Faransa

Kasashen Duniya sun ce babu bukatar Majalisar Dinkin Duniya a shirin afkawa Syria

Sabbin bayannan dake fitowa daga gwamnatocin kasashen yammacin Duniya da suka hada da Faransa da Burtaniya da Amurka na nuna cewar kasashen sun bayyana cewar idan ana batun yin amfani da Makami mai Guba ga jama'a, to babu bukatar amincewar majalisar dunkin Duniya wajen daukar Matakin daya dace, domin ladabtar da gwamnatin kasar Siriya.

Shugaba Obama na Amurka da shugaba Hollane na Faransa
Shugaba Obama na Amurka da shugaba Hollane na Faransa
Talla

Dama dai kasashen Amurka da Faransa sun fito fili sun bayyana aniyarsu ta ladabtar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, sai dai akwai Rahotannin dake nuna cewar ko a kasar Amurkan ma akwai Amurkawa da dama da suka nuna rashin amincewa da matakin da kasashen ke shirin dauka kan Siriya.

Kasar Amurka tace a shirye dakarun ta suke dan kai hari Siriya da zaran shugaba Barack Obama ya bada umurnin yin haka.

Shi kuwa shugaban kasar Fransa, Francois Hollande cewa yayi basu da kokanton zargin da ake yiwa Sirya na amfani da Makami mai Guba ga al’ummar kasar gaskiya ne, kuma dole a koyawa Siriya Hankali.

Bincike dai ya nuna cewar mafi yawancin Amurkawa basa goyon bayan wannan matakin da gwamnatin shugaba Barack Obama ke shirin dauka.

Kasar Israela babbar abokiyar kawancen Amurka na can tana kimtsawa da kuma kara karfafa tsaro a yankunan kan iayakar kasar da makwabtan kasashe, abinda ke alamta cewar da kyar ba'a fafata ba.

Sai dai akwai rade-radin dake nuna cewar shugaba Barack Obama na huskantar kasadar Siyasa muddin bai dauki mataki kan kasar Siriya ba.

Yanzu haka dai gwamnatin shugaba Obama ta daura Damarar kai farmakin Soji a kasar Siriya, abinda masu lura da al’amurra da dama ke kallo a matsayin abinda ba wani tasiri maras kyau zai yi ga shugaban kasar kasar Amurka ba, muddin dai Amurka ta takaitar da shi.

Amma inji masu lura da al’amurra shugaba Bashar al-Assad na iya kekasa Kasa ga wannan matakin Sojin da Amurka ke shirin dauka akan shi na zargin amfani da Makami mai Guba.

Tun bayan fidda Rahoton dake zargin Sojin gwamnatin Assad da amfani da Makami mai Guba a Siriya dai ne, gwamnatocin kasa-da-kasa suka yita bayyana matsayin su kan wannan matsalar.

Itama dai Majalisar dunkin Duniya ta yi tir da wannan al’amari, daya hallaka Daruruwan Mutane lokaci guda.

Gwamnatin shugaba Assad dai ta bayyanawa duniya cewar ba ta da Hannu ga harba Makami mai Guba ga al’ummarta, harma ta fidda shaidun dake nuna cewar ‘yan tawaye ne suka kai wannan harin.

Amma duk da Ikrarin gwamnatin, Turawan yammacin Duniya na ci gaba da amincewa da abinda ‘yan tawayen masu samun taimakon Turawan ke fada masu.

Kasashen Iran da Rasha duka dai sun bayyana rashin amincewa da zargin da ake yiwa Sojin gwamnatin Assad, harma suna masu bayyana kashedin su ga Turawan yammacin Duniya da cewar zasu takalo babban Bala’I ne kurum ga Duniya.

Iran dai ta sha bayyanawa Amurka cewar bata amince da mamayar kasar Siriya ba, harma tana iya daukar kowane irin mataki kan hakan. Bisa dukkanin alamu dai sai an gwabza fada mai daukar girma ya dauka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.