Isa ga babban shafi

Ziyarar Obama a Afrika karo na biyu

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama zai fara ziyara wasu kasashen Nahiyar Afrika a karo na biyu, inda zai ziyarci kasashen Senegal, Afrika ta kudu da Tanzania, akan batutuwan da suka shafi bunkasa demokradiya, zuba jari da kuma huldar diflomasiya.

Hoton Shugaban Amurka Barack Obama da shugaban Senegal  Macky Sall da wani ya zana yana ma shugaban maraba a ziyarar da zai kawo a kasashen Afrika
Hoton Shugaban Amurka Barack Obama da shugaban Senegal Macky Sall da wani ya zana yana ma shugaban maraba a ziyarar da zai kawo a kasashen Afrika REUTERS/Joe Penney
Talla

Shugaba Obama zai fara ziyarar ne a ranar Laraba kuma zai fara yada zango ne a kasar Afrika ta Kudu da cikin juyayin rashin lafiyar tsohon shugabansu Nelson Mandela.

Shugaban kasar Africa ta Kudu Jacob Zuma yace rashin lafiyar Nelson Mandela ba zai hana su karban bakuncin Barack Obama ba.

A lokacin da ya ziyarci kasar Ghana a shekarar 2009, shugaba Obama ya bayyana cewa yana da jinin ‘yan Afrika, kuma rayuwar shi na tattare da nasarori da matsalolin da Nahiyar ke fuskanta.

Masu bai wa shugaba Obama shawara suna ganin ya kamata hukumomin Washington su kara karfafa dangataka da kasashen Afrika, Kamar yadda mataimakin mai bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Ben Rhodes yace har yanzu ba su ba Nahiyar Afrika muhimmanci ba.

Sai dai jami’an gwamnatin Amurka suna sane da cewa harkokin tattalin arziki da makamashi da ke nahiyar, sun fara jan hankulan sauran kasashen da ke gasa da Amurka kamar su China.

Wannan ne karo na biyu, da shugaba Obama ke kawo ziyara Nahiyar Africa, ba tare da ziyarar Najeriya ba, duk da cewa Najeriya ce babbar kasa a Nahiyar, da kuma ake kwatanta ta da Afrika ta kudu wajen bunkasar tattalin arzikin kasa.

Obama zai kawo ziyarar ne ba tare da ya bakunci tushen shi ba kasar Kenya, duk da an samu sauyin gwamnatin Demokradiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.