Isa ga babban shafi
Amurka

Angelina Jolie ta dauki matakan kaucewa kamuwa da cutar sankarar mama

Tauraruwar Fim a Hollywood Angelina Jolie ta dauki matakan yin tiyata har sau biyu domin kaucewa kamuwa da cutar Sankarar Mama bayan likitanta ya gano tana dab da kamuwa da cutar.

Tauraruwar Fim Angelina Jolie  tare da Mahaifiyarta Marcheline Bertrand
Tauraruwar Fim Angelina Jolie tare da Mahaifiyarta Marcheline Bertrand REUTERS/Fred Prouser
Talla

A wata hira da jaridar New York Times ta Amurka, Angelina tace Likitanta ya kiyasta yiyuwar zata iya kamuwa da cutar sankarar Mama da kashi 87 da kuma cutar Sankarar Mahaifa da kashi 50.

“ Na yi kokarin na rage barazanar kamuwa da cutar” a cewar Angelina.

Angelina da ke da ‘ya’ya guda shida tace cutar Sankara ce ta yi sanadiyar mutuwar mahaifiyarta. Kuma an yi nasarar kwalkwale mamanta domin magance matsalar.

Yanzu haka kuma Angelina ta samu nasarar rage yiyuwar kamuwa da cutar daga kashi 87 zuwa kashi biyar, tana mai godewa Mijinta.

Angelina ta yi kira ga Mata suna da dama su dauki matakai domin kaucewa kamuwa da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.