Isa ga babban shafi
Kirista

Mabiya Addinin Kirista suna gudanar da Bikin Kirsimeti

A Ranar Ashirin da biyar ga watan Disamba ne, mabiya Addinin Kirista a sassa daban-daban na duniya ke gudanar da bikin kirsimeti, domin murnar tunawa da ranar haihuwar Yesu da suke bautawa.

Taron Mabiya Addnin Kirista a Bethlehem kasar Isra'ila
Taron Mabiya Addnin Kirista a Bethlehem kasar Isra'ila REUTERS/Ammar Awad
Talla

Daruruwan Mutane ne daga sassan daban daban suka kai ziyara Bethlehem inda aka bayyana anan ne aka haifi Yesu.

A Bethlehem, limamin Darikar Katolika a birnin Kudus ya bayyana goyon bayansu ga samun ‘Yancin Falesdinawa.

Fafaroma Benedict shi ne ya jagoranci taron mabiya a Majami’ar St Peter yana mai kira ga Mabiya Kirista su tsarkake zukatansu tare da neman gafara ga zunuban da suka aikata a baya.

Fafaroma Benedict ya yi addu’ar samun zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falesdinawa tare da neman zaman lafiya a kasashen Lebanon da Syria da kuma Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.