Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Sharhin Jaridun duniya akan nasarar Hollande a Faransa

Hankalin jaridun kasashen Duniya baki daya ya karkata ne akan nasarar da Francois Hollande ya samu a zaben Faransa bayan kayar da Nicolas Sarkozy. Jaridun Turai da Kasashen Duniya sun bayyana nasarar Francois Hollande, a matsayin wani sabon babi, amma sun yi gargadi akan kalubalen da ke gaban shi. 

Jaridun kasashen Duniya game da shan kayen Nicolas Sarkozy.
Jaridun kasashen Duniya game da shan kayen Nicolas Sarkozy. DR
Talla

Jaridar Daily Mail ta Birtaniya, ta buga babban labarinta inda take cewa, ‘’Au revoire President Blin Bling’’, yayin da Jaridun kasar Jamus ke damuwa kan yadda nasarar zata shafi dangantaka tsakanin Jamus da Faransa.

Jaridar Financial Times ta Jamus, tace nasarar Hollande, wani sabon babi ne ga shugaba Angela Merkel, inda Jaridar tace, Merkel ta yi duk yadda zata yi don ganin Sarkozy ya kai ga nasara, amma kuma wanda bata so shi ne ya kai ga nasara.

Jaridar tace, adawar Merkel ga Hollande, zai sa su raba hannun riga a kungiyar kasashen Turai.

Jaridar Tagesspiegel, tace zuwan Hollande zai zama babban kalubale ga Merkel, domin idan aka sake samun matsalar kudin euro, Jamus kadai ba zata iya magance shi ba.

Jaridar Independent ta Birtaniya, tace zuwan Hollande zai kawo sauyi kan yadda Turai zata magance matsalar basusukanta, da kuma yadda Faransa zata taka rawa a duniya.

Ita kuwa Financial Times ta Birnin Landon, cewa ta yi Sarkozy ya zama shugaba na hudu da matsalar tattalin arziki ta yi gaba da shi.

A nata bangaren Jaridar El Pais ta kasar Spain, tace an sake haifar gurguzu a Faransa ranar 6 ga wata.

Jaridar Global Times ta China, tace zuwan Hollande ba zai zama wani mizani na magance matsalar basusukan Faransa ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.