Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya zubar da mutuncin Faransa, inji Hollande

A wata hira ta musamman da François Hollande ya yi da RFI da France 24, dan takarar shugaban kasar Faransa yace ya yaba da kokarin shi a muhawarar da ya yi da Sarkozy tare da sukar gwamnatin Sarkozy ta raba Faransawa.

François Hollande, Dan takarar Shugaban kasa mai hamayya da Sarkozy  karkashin Jam'iyyar gurguzu ta socialist a lokacin da yake tattaunawa da wakilan Rediyo Faransa RFI da Gidan Telebijin na France 24
François Hollande, Dan takarar Shugaban kasa mai hamayya da Sarkozy karkashin Jam'iyyar gurguzu ta socialist a lokacin da yake tattaunawa da wakilan Rediyo Faransa RFI da Gidan Telebijin na France 24
Talla

“Ina tunanin an gudanar da muhawar yadda na yi tunani”, inji Hollande, wanda ya amsa ya samu faduwar gaba kafin tabka muhawar saboda daruruwan mutanen da zasu kalli muhawarar da aka nuna ta kafar Telebijin kai tsaye.

Muhawarar ranar Laraba ita ce ta farko kuma ta karshe amma tun da farko Sarkozy ya bukaci a gudanar da Muhawara sau uku amma Hollande ya ki amincewa.

‘Yan takarar guda biyu sun kwashe akalla sa’o’I uku suna musayar yawu akan batun tsare tsaren Tattalin arziki da shige da fice.

Bayan kammala Muhawar, Jaridun kasar Faransa sun ce kunnen doki aka yi tsakanin ‘Yan takarar, kuma hakan ya karya tasirin Sarkozy wanda tun da farko ya yi imanin zai iya canza ra’ayin Faransa ta hanyar Muhawara tsakanin shi da Hollande wanda aka yi hasashen zai lashe zaben shugaban kasa.

A wata hira ta hadin gwiwa tsakanin gidan Telebijin na France 24 da Rediyon Faransa RFI, Hollande yace gwamnatin Sarkozy ta raba Faransawa a shekaru biyar.

Sai dai babu wani banbanci tsakanin manufofin Hollande da Sarkozy akan batun dangantakar Faransa da kasashen duniya musamman akan batun Nukiliyar Iran da rikicin Syria da rikicin Isra’ila da Falesdinawa.

Amma dan takarar yace Sarkozy ya kada mutuncin Faransa a idon duniya.

Hollande ya sha alwashin zai kare mutuncin Faransawa tare da daukaka harshen Faransanci da al’adunsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.