Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Syria ta amince da yarjejeniyar zaman Lafiya, inji Annan

Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, kuma Mai shiga tsakanin rikicin kasar Syria, ya shaidawa kwamitin Sulhu cewa, Syria ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya da zata fara aiki daga ranar Goma ga watan Afrilu.

Kofi Annan, Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya wanda ke jagorantar  sasanta rikicin kasar Syria
Kofi Annan, Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya wanda ke jagorantar sasanta rikicin kasar Syria
Talla

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Turai suna kokwanto game da wannan alkawarin da kasar Syria ta dauka domin samun zaman lafiya.

Gwamnatin Kasar Amurka tace zata taimaka wa masu binciken rikicin Syria da kudi Dalar Amurka Miliyan 1.25.

Majalisar Dinkin Dunya tace akalla sama da mutane 9,000 ne suka mutu tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al Assad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.