Isa ga babban shafi
Panama

Tsohon Shugaban kasar Panama Noriega na garkame yanzu haka bayan mayar da shi gida

Tsohon Shugaban kasar Panama Manuel Noriega na garkame yanzu haka akasar tasu, kwana daya rak da komawarsa kasar, bayan ya kwashe shekaru kusan 20 yana tsare a kasar Amurka da Faransa saboda safarar miyagun kwayoyi da halatta kudaden haram.  

Jirgin da ya mayar da tsohon Shugaban Panama Manuel Noriega zuwa gida daga birnin Paris
Jirgin da ya mayar da tsohon Shugaban Panama Manuel Noriega zuwa gida daga birnin Paris Reuters/Gonzalo Fuentes
Talla

Dangi da ‘yan uwansa sun yi ta murna saboda komawarsa kasar tasu, duk da cewa ana iya sakayeshi na wani tsawon lokacin.
 

Noriega ya mulki kasar ta Panama karkashin gwamnatin soja daga shekarar 1983 zuwa 1989, kuma kotun kasar ta same shi da laiguka uku, yayin da ya ke zaman gidan yari a kasar Amurka.

Ministan harkokin Cikin Gidan kasar ta Panama Roxana Mendez ta tabbatar da cewa ba a gidan kasaita za a ajiye Noriega ba, amma daga karshen wannan makon zai iya ganawa da baki da suka hada da iyalansa 'yan uwa da abokan arziki.

Manuel Noriega tsohon shugaban kama-karya na kasar Panama
Manuel Noriega tsohon shugaban kama-karya na kasar Panama REUTERS/Henry Romero

Ranar Lahadi data gabata aka mayar da Noriega gida daga birnin Paris na kasar Faransa inda ya ke zaman gidan wakafi, bayan an tisa keyarsa daga Amurka, yayin da ya kammala wani wa'adin na gidan fursuna.

Shugaban kasar ta Panama Ricardo Martinelli ya shaida wa manema labarai cewa tsohon Shugaban dan kama-karya Manuel Noriega, mulkin ya kawo karshe sakamakon kutsen da Amurka ta kai na kamo karshen shekarar 1989. Kuma ya kasance dan leken asirin Amurka na shekaru kafin ya zama Shugaban kasa, amma sun raba gari, lokacin da Amurka ta zarge shi da taikamawa masu hada hadar miyagun kwayoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.