Faransa-Panama
Kotun Faransa ta mika shari’ar Noriega zuwa Panama
Kotun daukaka kara a kasar Faransa, ta amince da shirin mayar da Tsohon shugaban kasar Panama, Manuel Noriega gida, domin zaman gidan yari kan laifukan da ya yi lokacin da ya jagoranci kasar.Tsohon shugaban, wanda a baya na hannun daman kasar Amurka ne, ya kwashe sama da shekaru 20 a gidan yarin kasar, kafin kai shi Faransa a bara, inda aka daure shi bisa laifin halatta kudaden haram.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: