Isa ga babban shafi
Denmark

Sojin Ruwan Denmark sun tarwatsa jirgin ‘yan fashi a tekun Somaliya

Sojin ruwan Denmark Sun cafke wani jirgin ‘yan fashi dake dauke da makamai a mashigin ruwan tekun somaliya, inda suka cafke yan fashi shida tare da nutsar da jirgin. Kodayake kakakin rundunar sojin ya bayyana sakin ‘yan fashin.“ basu aikata wani mummunan laifi a tekun ba, illa dai suna cikin jirgin ne da ke dauke da makaman da za’a iya gudanar da fashi lokacin da bai dace ba”. Tabakin kakakin rundunar sojin ruwan ke nan Kenneth Nielsen.An dade dai ana fama da fashin jirage a wannan yankin tekun na Somaliya dake gabacin Africa, wanda hakan ya dade yana kawo cikas ga jiragen da ke jigila tsakanin turai da Asiya.  

Mashigin Tekun somaliya
Mashigin Tekun somaliya Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.