Isa ga babban shafi
Girka

Sakamako kan mutuwar yan jarida a duniya

Kungiyar PEC mai zaman kanta ,da ke kokowa da kare hakin yan jarida a duniya ,ta gudanar da wani bincike ,wanda ta sanar da sakamakon shi a yau ,in da ta gano cewa ,yan jarida 90 su rasa rayukansu a kan aiki a cikin kasashen duniya tun farkon wanan shekara ta 2010. Sakamakon ya nuna da cewa an samu raguwar kashe –kasshen yan jaridar da kishi 25 cikin 100, idan aka dangantashi da na shekarar da ta gabata ta 2009.Blaise Lempen, babban magatakarda na kungiyar ta PEC ,ya furuta cewa babu wani cigaba da ake samu,sai dai koma baya a kan lamarin gudanar da aikin jarida ba tare da fuskantar wani tashin hankali ba a duniya.Kasashen da sakamakon ya nuna, sun hada Mexico ,Iraki ,Rasha,Nepal,Najeriya ,Colombia,Thailand, Angola ,India ,Ouganda Venezuela da dai sauren su.Fatan karshe shi ganin komi ya daidaita a shekara mai zuwa.  

Aikin Jarida na fuskantar kalubale a duniya
Aikin Jarida na fuskantar kalubale a duniya AFP/Alex Wong
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.