Isa ga babban shafi
Greece

Ma’aikatan Jirgin kasa sun shiga yajin aiki a kasar Girka

A yau laraba ne ma’aikatan Jirgin kasan kasar Girka suka shiga yajin aiki danagane da koken da suke yi ga gwamnatin kasar kan kudinrinta na sauya al’amurran da suka shafi matukan jirgin wanda ya dabaibaye gwmantin kasar da bashin kudin Euro Bilyan goma.Ma’aikatan sun fara yajin aikin ne da yammacin yau inda suka yi gangami don nuna adawa ga kudirin gwamnati, yajin aikin da kuma suka bayyana zai zarce zuwa tsawon mako daya.Gwmanatin kasar dai ta kudiri aniyar sauya tsarin kamfanin kula da jirgin kasar ne na OSE wanda ke cike da matsaloli na sama da fadi da mundahana a kasar. Sauya al’amurran dai yana daga cikin sabon tsarin da gwamnatin kasar ta dauka na farfado da tattalin arzikin kasar bayan da ta samu agaji daga kungiyar Tarayyar Turai da hukumar bada lamuni ta duniya a watan Aprairu. Ma’aikatan sun bayyana cewa Gwamnatin kasar ke da alhakin dukkanin matsalolin bashin da ke addabar kamfanin na OSE, kamar yadda suka bayyana cewa shekaru da dama ne gwamnatin ta tursasawa kamfanin hada hannu da ‘yan siyasa.Kudirin gwamnatin dai a halin yanzu shi ne wargaza dukkanin tsarin kamfanin da nufin mika al’amurran kamfanin ga masu saka hannun Jari  

Yajin aikin kasar Girka da aka taba gudanarwa a watan Yuni
Yajin aikin kasar Girka da aka taba gudanarwa a watan Yuni Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.