Isa ga babban shafi
Faransa-Hijab

Majalisar Dattijai Ta Amine Da Haramtawa Mata Niqabi da Burqa

Wakilan majalisar Dattawan kasar Faransa sun rattaba hannu kan dokan haramtawa mata sanya hijab dake rufe fuska cikin jamaa.Haramcin zai fara aiki ne daga sabuwar shekara mai zuwa, idan har Majalisar Tsarin mulkin kasar ta amince.Wakilai 246 ne suka amince da fara aiki da dokan, yayin da Wakili daya bai goyi bayan dokan ba.Ana bukatar Majalisar Tsarin Mulkin kasar ta zartas  kafin shudewar wata daya.Karamar Majalisar kasar ta rigaya ta amince da a fara aiwatar da  Dokan tun cikin watan bakwai daya gabata.Dokan bai tabo addinin musulunci ba.Gwamnatin Shugaba Nicholas Sarkozy ta nace da neman fara aiki da Dokan saboda hana matan kasar koyi da tsarin addinin musulunci.Idan aka fara aiki da Dokan za'a dibi watanni shida ana fadakar da matan kasar domin su kyamaci amfani da tufafin dake rufe fuska.Maccen da ta saba dokan za'a ci taran ta kudin Turai, Euro 150 ko horon sanin makaman zama dan kasa na gari.  

Wasu mata musulmi sanye da niqab
Wasu mata musulmi sanye da niqab rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.