Isa ga babban shafi

Sabon rikici tsakanin mayakan kurdawa da dakarun Syria ya kashe mutane 25

Wani sabon fada da ya barke tsakanin dakarun gwamnatin Syria da mayakan Kurdawa da ke arewacin kasar ya hallaka mutane 25 cikin kwanaki biyu kachal.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun rikici tsakanin bangarorin biyu ba
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun rikici tsakanin bangarorin biyu ba AP - Hassan Ammar
Talla

Tun farko mayakan na kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka ne suka fara kaddamar da hari kan dakarun soji a yankin Dheiban, sai dai sun yi ikirarin gungun ‘yan ta’adda ne suka tarwatsa, lamarin da ya tashi rikicin da aka fara shi tun daren Lahadi.

Ko a farkon watan nan sai da makamancin fadan tsakanin bangarorin biyu yayi sanadin mutuwar mutane 90, bayan kwashe kwanaki 10 cir suna gwabzawa da juna.

Wata kungiya da ke yaki da cin zarafin dan adam a Syria ta ce wannan sabon fada yayi kama da ramuwar gayya, la’akari da yadda dakarun sojoji suka fara kaiwa mayakan na kurdawa hari a rikicin na farkon watan da muke ciki na Satumba.

Kungiyar ta ce a dai-dai lokacin da rikicin ke kara kazancewa a yau Talata, na gano cikin mutanen da suka mutu har da mace guda daya.

Rahotanni sun nuna cewa mayakan na kurdawa sun jefawa sansanin sojojin bam, kafin daga bisani su bude musu wuta, sai dai ba tare da bata lokaci ba dakarun suka mayar da martani.

Kungiyar ta ce irin wannan rikici da ke barkewa a yankin tsakanin bangarorin biyu lokaci zuwa lokaci ya lakume rayukan dubban mutane

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.