Isa ga babban shafi

Wani hadarin mota ya kashe mutane 50 a Pakistan

Akalla mutane 51 ne suka mutu a wani mummunan hadarin mota da ya auku a kudu maso yammacin garin Balochistan na Pakistan, bayan da wata mota makare da fasinjoji ta fado daga kan gadar da ta ke tafiya. 

Wani hadari a Pakistan.
Wani hadari a Pakistan. REUTERS - STRINGER
Talla

Tun farko dai Motar dauke da fasinjoji sama da 40 ce ta kwace daga hannun matukin ta ta afka kasan gada sannan ta danne wani kwale-kwale da ke dauke da dalibai ‘yan Firamare. 

Bayanin da jami'an tsaro suka bayar sun ce alakanta da hadarin da ko dai gudun wuce sa'a ko kuma bacci ne ya dauki direban motar lamarin da ya sa ta kwace ta kuma fada kasan gadar. 

Har yanzu dai akwai sauran mutane 9 da ba’a kai ga gano gawarwakin su ba, kuma a karin bayanin da ya yi, guda daga cikin jami’an gwamnatin da suka ziyarci inda lamarin ya faru Hamza Anjum ya ce gawarwaki 42 da aka samo yanzu sun yi lalacewar da an kasa gane ainahin mutanen saboda yadda suka sha ruwa suka kumbura, har fatar jikinsu ta salubewa. 

Jami’an bayar da agajin gaggawa na kasar sun ce bayan yawan mutanen da motar akwai kuma lodin kayayyaki wanda ya yi wa motar yawa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.